1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta saki ragamar mulkin Zirin Gaza

Mohammad Nasiru Awal ZMA
October 3, 2017

Karkashin jagorancin Rami Hamdallah majalisar ministocin Falasdinawa ta yi zama karo na farko a birnin Gaza tun shekarar 2014.

https://p.dw.com/p/2l9lt
Gaza-Streifen Besuch von Palästinenser Premierminister Rami Hamdallah
Firaministan Falasdinawa Rami Hamdallah lokacin ziyarar da ya kai Zirin GazaHoto: Reuters/M. Salem

Majalisar ministocin Falasdinawa karkashin jagorancin Firaminista Rami Hamdallah ta yi zama a birnin Gaza karo na farko cikin shekaru uku. Hamdallah ya jaddada kudirinsa na kawo karshen gwagwarmayar neman rike madafun iko tsakanin kungiyar Hamas da ke mulki a Zirin Gaza da hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinu da ke Yammacin Kogin Jordan.

Yanzu haka dai kungiyar Hamas ta mika ragamar mulkin Zirin Gaza ga gwamnatin Falasdinu karkashin Shugaba Mahmud Abbas na kungiyar Fatah mai sassaucin ra'ayi.
 

A ranar Litinin Rami Hamdallah ya jagoranci wata tawagar mutum 120 daga Yammacin Kogin Jordan zuwa Gaza. Tun shekarar 2006 ba a gudanar da zaben majalisar dokoki a yankunan cin gashin kai na Falasdinawa ba.

A shekarar 2007 Hamas, wadda kungiyar EU da kasar Amirka da kuma Isra'ila suka sanya ta a jerin kungiyoyin ta'adda, ta yi amfani da karfi ta karbe wa kanta ragamar mulki a Zirin Gaza.