Halinda ake ciki a Gaza bayan tsagaita wuta
November 22, 2012Sanar da tsagaita wuta ke da wuya, sai Palasdinawan zirin Gaza suka bazama kan tituna don shagulgulan murnar abin da suka kira "Nasarar da suka yi ta gagarar makiya" duk da rasa rayukan yan uwansu 160 da sukai da jikkatar daruruwa.
Titunan zirin na Gaza, wanda kwanson makaman da jiragen isra'ila suka yi ta harbawa ke warwatse kansu, sun cika makel da daruruwan masu shagulgulan kawo karshen hare haren kwanaki takwas da Isra'ila ta kai kan zirin na Gaza
Masu bukukuwan da suka daga tutocin kungiyar Hamas da hotunan wadanda suka kwanta dama sakamakon har haren, sun ce wannan biki na dukkan larabawa da musulmin duniya ne dama illahirin al'umomin da ke fuskantar danniyya.
"Tada kayar baya, da kin mika wuya ga azzalimai shi ya sa ake ganinmu da kima a idanun duniya, mu a wajenmu da kaskanci gwanda shahada, kuma da yardarm Allah sai mun kwato masallacin Kudus da Isra'ila ta mamaye munyi sallah cikinsa"
Su kuwa wadanda yakin ya jefa cikin halin kakani ka yi, ko kuwa suka rasa danginsu, wadannan shagulgula da ake yi bai hanasu ci gaba da yin makaoki da la'antar wadanda suka yi wa danginsu sanadi ba.
Kamar dai yadda Isra'ilan ke ikirari, hare haren nata sunyi nasarar ragargaza illahirin karfin makaman kungiyoyi masu tada kayar baya dake zirin na Gaza, ikirarin da jagororin Hamas suka musanta. Suna masu cewa, har yanzu rumbun makamansu nanan cike makel da makaman da kasar Iran ta basu, da kuma wadanda suka kera da kansu, kuma a shirye suke da su sake fafatawa da Isra'ilan a duk lokacin da ta takale su.
Ana su bangaren, masu tsatsauran ra'ayi na bani Yahudu na ganin cewa, gwamnatin Natayanhu ta basu kunya da ta ba da kai bori ya hau, har ta yi sulhu da Hamas.
" Ada an mayar da Hamas saniyar ware, amma tun da aka fara yakin na sai muka ga yawancin kasashen duniya na sake tausaya mata, kai har wasu shuwagabannin larabawa ma suka yi ta kai mata ziyara, kamar yadda muka yadda da tattaunawa da ita a fakaice, dole ne ma a yanzu Hamas ta dauki kanta a matsayin gwarzon kasashen larabawa"
Kamar dai yadda masharhanta ke gani, bawa Palasdinawa kasar kansu, da kuma taimaka musu da isassun makamai shine kadai zai iya magance irin ta'annutin da Isra'ila ke musu.
Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Usman Shehu Usman