1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rashin sanin tabbas a tsakiyar Afirka

January 4, 2013

Duk da kokarin sasantawa tsakanin shugaba Bozize da 'yan tawayen Seleka, har yanzu ana cikin zaman zullumi a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ma makwabciyarta Kongo.

https://p.dw.com/p/17DrP
Hoto: dapd

A wannan makon ma jaridun na Jamus sun yi tsokaci a kan batutuwa da dama a nahiyar Afirka, sai dai halin da ake ciki a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fi daukar hankalin akasarin jaridun na Jamus. A labarin da ta buga a kan kasar, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa.

"Shugaba Francois Bozize ya shiga halin tsaka mai wuya, bayan 'yan tawaye sun yi watsi da kiran da ya yi na su kyale shi ya cika wa'adin mulkinsa da ya saura shekaru uku. Jaridar ta ce shugaban wanda shi ma ya hau kan kujerar mulki a wani juyin mulki a shekarar 2003 yana kara shan matsin lamba daga kawancen 'yan tawayen Seleka, kasancewa a baya ya sha ta da alkawuran da yayi musu, a wannan karon ma ba su ga wani abin da zai canza ba. Shugaban dai ya rasa abokan dasawa, domin duk da rokon da yayi, Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka, ta ce ba za ta tura sojoji da za su yi kasalanda a kasar ba. Faransa dai a karkashin sabon shugaba Francois Hollande tana bin wata manufa ta takatsantsa ga Afirka. Ita kuma Amirka wadda ke da sojoji a kasar to amma dakaruntan na tafiyar da wani aiki ne na farautar madugun 'yan tawayen kasar Uganda Joseph Kony da ake zargi da aikata laifukan yaki."

An sake tayar da wani tsohon rikici a tsakiyar Afirka inji jaridar Der Tagesspiegel sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Zentralafrika Soldaten in Bangui
Kasashe makwabta na tura sojoji birnin BanguiHoto: dapd

Rikicin tawaye ya mamaye tsakiyar Afirka

"Bayan rikicin da aka yi fama da shi a gabacin Kongo a watan Nuwamban shekarar 2012, yanzu makwabciyarta wato Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta zama wani fagen daga na bore wanda ya shafi rayuwar fararen hular kasar. Jaridar ta ce da mamaki, barkewar sabon rikicin, domin kimanin mako guda da ya gabata magana ake game da cimma wani kwarkwaryar shirin tsagaita wuta a tattaunawar zaman lafiya da ta gudana a makwabciyar kasar wato Chadi tsakanin marikitan. Ko da yake shugaba Bozize ya nuna shirin ci-gaba da tattaunawa bisa sharadin cewa 'yan tawayen su janye daga yankunan da suka kama."

Koma baya ga shirin zaman lafiyar Kongo

Majalisar Dinkin Duniya ta kawo cikas ga shirin zaman lafiya inji jaridar Die Tageszeitung. Ta ce:

"jim kadan gabanin komawa zagaye na gaba na tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Kabila da 'yan tawayen kungiyar M23 a kasar Uganda, Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa 'yan tawayen takunkumin hana tafiye tafiye da sayar musu da makamai da kuma dora hannu kan asusun ajiyarsu. Hakazalika Majalisar ta kuma kakaba wa kungiyar 'yan tawayen Hutun Rwanda wato FDLR takunkumi. Sai dai wannan matakin ya zo a wani lokacin da bai dace ba, kasancewa a wannan Juma'a aka koma teburin shawarwari tsakanin gwamnatin Kongo da kungiyar ta M23 a Uganda, karkashin wani shirin samar da zaman lafiya da kasashen yankin suka tsara. Kuma saboda alkawarin yin wannan zama, kungiyar M23 ta janye daga garin Goma a karshen watan Nuwamba, bayan mamaya ta tsawon kwanaki 10. A ranar tara ga watan Disamba aka fara tattaunawar amma saboda hutun kirsmetti aka dage shi zuwa hudu ga watan Janerun wannan shekara ta 2013. Bisa ka'aidojin takunkumin da bai kamata Uganda ta ba wa 'yan tawayen izinin shiga kasar ba."

Kongo M23 Rebellen ziehen aus besetzen Gebieten
Ko da yake sun janye daga Goma, amma sojojin M23 ba sa nesa da garinHoto: AP

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi