Halin da ilimi ke ciki a Najeriya da Nijar | Zamantakewa | DW | 16.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Halin da ilimi ke ciki a Najeriya da Nijar

A kasashe masu tasowa da dama, ana fuskantar kalubale kala-kala a fannin ilimi. Haka lamarin yake a kasashen Tarayyar Najeriya da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar.

Nigeria Jangebe 300 Schulmädchen von bewaffneten Männern entführt

Makarantun Najeriya na fuskantar barazanar tsaro

Sau da dama, ana fuskantar kalubale a fannin ilimi musamman a kasashe masu tasowa. A Jamhuriyar Nijar da Tarayyar Najeriya, matsalolin tsaro na taimakawa wajen samun koma baya a fannin ilimi musamman na makarantun firamare da sakandare. A baya-bayan nan dai, ana ta kwashe daliban makarantun firamare da sakandare har ma da jami'o'i a jihohin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A baya ma dai an samu irin wannan matsalar a yankin Arewa maso Gabashin kasar daga 'yan ta'adxdan Boko Haram, sai dai lamarin ya fi kamari a yanzu haka a yankin Arewa maso Yamman da 'yan bindiga suka taso gaba. Ana dai alakanta wadannan matsaloli da yawan faduwar jarrabawa da ake samu daga dalibai, musamman jarrabawar kammala sakandare da ta shiga jami'a.

Sauti da bidiyo akan labarin