1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Sudan Ta Kudu

January 13, 2014

Duk da nasarorin da sojojin gwamnati suka samu, inda suka karɓe wurare da dama a yaƙin basasar Sudan ta Kudu, mayaƙan 'yan tawaye suna ci gaba da riƙe gari ɗaya mai muhimmanci a ƙasar.

https://p.dw.com/p/1Apn6
Hoto: Reuters

Har yanzu ba'a ga alamun kawo ƙarshen mummunan halin da ɗimbin 'yan gudun hijira da mazauna Sudan ta Kudun suke ciki ba. Wasu 'yan gudun hijiran sun yi asarar rayukansu, dubbai kuma sun rasa duk abin da suka mallaka tare da tsoron ci gaba da ƙazamin yaƙi a ƙasar.Luoy Kuong yana cikin wani hali na kiɗimewa da mummunan tashin hankali. Mazaunin na garin Bentiu ya fito ƙofar gidnsu, ko a ce abin da ya taɓa zama ƙofar gidan da yanzu aka rushe shi ya zama turbaya. A kewayen da ke makwabtaka da Kuong, 'yan gidaje ƙalilan ne suke tsaye, kuma ko su ɗin ma, sai da 'yan kwasar ganima suka wawashe duk abin da ke cikin su. Kuong yace:

''Garin namu sai dai kawai ayi shiru. Babu wani abin da zan iya cewa. Duk abin da ke nan kewaye damu an kone shi kurmus.Saurayin dan shekaru 18 da haihuwa yace bai ma san inda sauran iyalinsa suke ba, bai kuma san abin da zai yi ba, ko abin da zai zama makomarsa nan gaba.''

A kewayen gidan Luoy Kuong ma an rushe kusan gidajen gaba ɗaya, sai 'yan kalilan, wadanda ke tsaye bayan masu kwasar ganin sun auka masu. Garin Bentiu, babban birnin lardin Unity mai arzikin man fetur, yanzu dai ya watse babu kowa cikinsa. A gefen tituna babu komai sai gawarwarkin sojoji da farar hula da yaƙin basasan ya rutsa da su. A bayan ɗauki ba daɗi mai tsanani, sojojin gwamnati ranar Jumma'a suka sake ƙwace wannan gari daga hannun mayaƙan 'yan tawayen ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar, waɗanda watan Disamba suka mamaye shi. Wani mayaƙi da ke biyayya ga rundunar sojan SPLA anji yana cewa:

Südsudan Luoy Kuong aus Bentiu
Garin Bentiu an rushe shi ya zama turbayaHoto: DW/A. Kriesch

''Yanzu dai komai na hannunmu. Babu wani abin tsoro da zai iya faruwa nan gaba. Al'ummar farar hula suna iya komawa wuraren zamansu.''

To sai dai wannan alƙawari ne da mafi yawan mazauna garin na Bentiu ba su amince da shi ba, saboda kusan 'yan garin gaba ɗaya sun tsere zuwa sansanonin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tanadar, inda suke neman tsira bayan da 'yan tawaye suka jefa yankin gaba ɗayansa cikin ruɗami.

Tun daga ranar uku ga watan Janairu na wannan shekara ɓangarorin biyu masu yaƙi da juna suke tattaunawa ta neman zaman lafiya ta hanyar mai shiga tsakani a Addis Ababa, babban birnin Habasha. Shugaban yan tawaye Riek Machar ya ce sharaɗinsa na tsagaita buɗe wuta shi ne sakin duka fursunonji 11 magoya baynsa da aka kama, waɗanda aka zarge su da laifin haɗa baki domin ƙoƙarin aiwatar da juyin mulkin kayar da shugaban ƙasa Salva Kiir. Shi kansa Salva Kiir ya ƙi yarda da wannan buƙata, yayin da Riek Machar ya musunta an taɓa wani yunƙuri na juyin mulki. Tattaunawar dai ta ƙasa samun ci gaba yayin da duk ƙoƙarin da aka sha yi daga ƙetare domin sulhunta mutanen biyu yaci tura.

A daura da haka, ko wane ɓangare yana ƙoƙarin ganin ya kafa kansa ta hanyar amfani da ƙarfin soja a ƙasar ta Sudan ta kudu, yayin da al'ummar farar hula suke ci gaba da kasancewa cikin mummunan hali. A bisa kiyasin MDD, mutane fiye da 200.000 suka tsere a matsayin yan gudun hijira. Kakakin rundunar sojan Sudan ta kudu, Philip Aguer dake hira da tashar DW yace:

Südsudan Kämpfe Riek Maschar ARCHIVBILD 2007
Shugaban yan tawayen Sudan Ta Kudu, tsohon mataimakin shugaban kasa Riek MacharHoto: Al-Haj/AFP/Getty Images

Wannan dai rikici ne na siyasa, to amma sai ga shi wasu daga cikin 'yan siyasarmu sun gaiyaci sojoji da niyyar su yi amfani da ƙarfi domin cimma ɓurinsu na samun mulki. Sulhunta wannan rikici ba yana tattare da amfani da ƙarfin soja ba ne, amma abin da muke yi shi ne mu taimaka domin sake ƙwato yankunan da 'yan tawayen suka mamaye. wannan shi ne aikin da aka ce mu yi, wanda kuma shi ne ke rubuce a ƙundin tsarin mulkin ƙasarmu. A ɗaya hannun, Peter Adwok, mai goyon bayan 'yan tawaye, ya yi zargin cewar tun da farko, sojojin gwamnati ba su da wata niyya illa ta tsabtace jinsi. Adwok watanni biyar da suka wuce ya yi asarar muƙaminsa na minista, a lokacin da shugaban ƙasa Salva Kiir ya rushe majalisar ministocinsa gaba ɗaya.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafa: Adrian Kriesch/Jan-Philipp Scholz/Umaru Aliyu

Edita: AbdulrahAmane Hassane