Halin cin-hanci da rashawa a duniya | Labarai | DW | 03.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin cin-hanci da rashawa a duniya

Transparency International ta ce Najeriya ce kasa ta 33 da aka fi cin hanci da karbar rashawa a cikinta a duniya, yayyin da Afghanistan da Somaliya ke kan gaba.

Kungiyar Transparency International ta fitar da rahotonta na shekara game da batun cin hanci da karbar rashawa, inda ta sanya Afghanistan da Koriya ta Arewa da kuma Somaliya a matsayin kasashen da suka fi fama da wannan mummunar dabi'ar. Sauran kasashen da suka fi cin hanci a duniya dai sun hada da Syriya da ke fama da rikicin siyasa, sai Libiya da Sudan da kuma Sudan ta kudu, yayin da tarayyar Najeriya ke a matsayi na 33. Kungiyar ta kuma nunar da cewa a nan Turai, kasar Girka da ke fama da karayar tattalin arziki ce ta fi cin hanci da karbar rashawa.

Alkaluman da Transparency International ta fitar sun nunar da cewa kasashen Danmark da kuma New-Zeeland ne suka fi kamanta gaskiya da adalci wajen tafiyar da harkokin da suka shafi dukiyar kasa da kuma mu'amalar tattalin arziki. Sauran kasashe da cin hanci da karbar rashawa bai yi katutu a cikinsu ba sun hada da Luxembourg da Canada da Australiya da kuma Holland.

Mawallafi: Garzali Yakubu
Edita: Umaru Aliyu