Sojan Faransa sun kashe wani jigo a kungiyar 'yan ta'adda
November 6, 2019Talla
Ministar tsaron kasar ta Faransa ta tabbatar da kisan shugaban kungiyar ta Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin a shafinta na Twitter, inda ta ce an halakashi ne tun a ranar tara ga watan jiya. Ali Maychou na daya daga cikin shugabannin kungiyoyin addini masu kaifin kishin Islama a Mali, Faransa na zargin Ali Maychou ne da hannu wajen kaddamar da hare-haren ta'addanci ga dakarun kasar da na Amirka har da na rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali.