Hadarin sojan Faransa a yankin Sahel | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 29.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Hadarin sojan Faransa a yankin Sahel

Jiragen sama masu saukar ungulu na sojan Faransa da suka yi karo yayin da suke shawagi na sintirin tsaro a Mali ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar 13.

Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten (Reuters/B. Tessier)

Sojan Faransa a bakin daga na farautar 'yan ta'adda a Mali

A labarin da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce labarin mutuwar sojojin Faransa 13 da ke aikin yaki da 'yan ta'adda a Mali ya girgizar kasar ta Faransa. Jaridar ta ce wannan shi ne karon farko tun bayan shekara 1983 da Faransar ta yi asarar sojoji masu yawa a lokaci guda. A 1983 sojojin kasar 58 suka rasu a wani harin bam da a birnin Beirut na kasar Lebanon. Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana sojojin da ke yakar 'yan ta'adda a Mali da gwarzaye wadanda burinsu shi ne su kare mu. Su dai sojojin wani bangare ne na rundunar nan ta musamman wato Barkhane da tun a wasu kwanakin da suka gabata suke fatattakar kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel. 

Jamus na goyon bayan Faransa na samun dauki daga EU 

Mali Soldaten der Malischen Armee und der französichen Barkhane-Streitkräfte (Getty Images/AFP/D. Benoit)

Sojojin Mali da Faransa na sintiri a Menaka

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci kan rashin sojojin na Faransa sakamakon taho mu-gama da jiragen saman masu saukar ungulu guda biyu suka yi tana mai cewa mutuwar sojojin 13 ya sa gwamnatin a birnin Paris ta kara daga murya na nema karin taimako a yakin da ake yi da 'yan tarzoma a yankin Sahel. Ta ce wannan kiran ya shiga kunnen gwamnatin tarayyar Jamus. Jaridar ta ce a ranar 11 gab watan Nuwamba shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kaddamar da sabon dandalin tunanwa tunawa da sojojin kasar da suka rasa rayukansu a lokacin aiki a ketare, sai ga shi a ranar 25 ga watan sojojin kasar 13 sun rasu sakamakon hatsarin jiragen alikopta a Mali. Sai dai kasar ta ce ba za ta sauya dubarun yakinta a yankin an Sahel ba, amma ta sake yin kira neman tallafi daga Kungiyar Tarayyar Turai. A nan Jamus ma ministar tsaron kasa Annegret Kramp-Karrenbauer ta goyi bayan wannan kira tana mai cewa tabbatar da tsaro a yankin Sahel wani bangare na tsaron kan nahiyar Turai. Sai dai a cewar jaridar har kawo yanzu gaskiyar batu shi ne kasar Faransa ce ke daukar nauyin mafi yawan aikin tsaro a yankin.

 Al'ummar Kwango na jin jiki da matsalolin tsaro 

Demokratische Republik Kongo Ausschreitungen in Beni (DW/J. Kanyunyu)

Kokarin kashe wutar bore a kasar Kwango

Jaridar Die Tageszeitung ta ruwaito cewa a gabashin Kwangon har yanzu sojojin gwamnati na fafatawa da 'yan tawayen kungiyar ADF, yayin da al'umar yankin ke jin jiki saboda wannan rikici. Ta ce wani kisan gilla da 'yan tawaye suka yi wa mutum takwas a birnin Beni ya sa hankurin mazauna yankin ya kare, inda suka yi wa sojojin Majalisar Dinkin Duniya bore, suka kuma yi kone-kone a birnin. Sai dai mutum biyu daga cikin masu zanga-zangar sun rasa rayukansu lokaci da sojoji suka bude wuta kan matasa da ek nuna fushinsu sakamakon halin tabarbarewar tsaro da yankin na gabashin Kwangon ke ciki. A farkon watan Nuwamba sabuwar gwamnatin Kwango ta fara kai sabbin hare-hare kan 'yan tawayen kungiyar ADF tun sannan kuma farar hula fiye da 75 aka kashe a hare-hare na adduna. Mazauna yankin dai na zargin cewa ba sa samun wani dauki daga sojojin Majalisar Dinkin Duniya da aka girke a birnin Beni.

Sauti da bidiyo akan labarin