Hadarin jirgin sama ya hallaka mutane biyu | Labarai | DW | 07.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin sama ya hallaka mutane biyu

Mutane biyu sun hallaka wasu da dama suka samu raunika sakamakon hadarin jirgin sama a Amirka.

Akalla mutane biyu sun hallaka yayin da wasu fiye da 180 suka samu raunuka, lokacin da jirgin sama da ke shirin sauka ya rikito, a filin saukar jiragen saman San Francisco na Amirka. Jirgin ya kama da wuta lokacin da ya fada, kuma fasinjoji sun yi amfani da kofofin fitar gaggawa, domin ficewa daga cikin jirgin.

Jirgin mallakin kamfanin Asiana na kasar Koriya ta Kudu, kirar Boeing mai lambar tafiya 777 yana dauke da mutane 307 lokacin da hadarin ya faru. Wannan ya zama karon farko da jirgin kamfanin ya yi hadari cikin tarihinsa na kusan shekaru 20.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas