Hadarin jirgin ruwa ya rutsa da daruruwan mutane | Labarai | DW | 16.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin ruwa ya rutsa da daruruwan mutane

Jirgin ruwan na Koriya ta Kudu ya nitse ne dauke da mutane kimanin 460 da ke kan hanyar zuwa tsibirin shakatawa na Jeju da ke kudancin kasar.

Masu tsaron kan iyakokin tekun kudu masu yammacin kasar Koriyar ta Kudu sun ce akalla mutane hudu sun rasu sannan 14 sun samu raunuka lokacin da wani jirgin ruwa da ke dauke da mutane kimanin 460 ya nitse a yankin. Rahotannin baya bayan nan sun ce an ceto mutane 164, kuma har yanzu ba a ga fasinjoji kusan 300 ba. Jirgin ruwan dai yana kan hanya ne daga birnin Inchon na gabar teku zuwa tsibirin shakatawa na Jeju da ke kudancin kasar ta Koriya ta Kudu lokacin da hadarin ya auku. Daga cikin fasinjojin jirgin akwai yaran makaranta fiye da 300 da ke kan hanyar zuwa balaguro.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe