Hadarin jirgin ruwa a kasar Pilipin | Labarai | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin ruwa a kasar Pilipin

Jirgin ruwan kasar ta Pilipin mai suna Le Kim Nirvana mai aikin jigilar fasinja a tsakanin wasu tsibiran kasar ya nutse yana dauke da mutane 189 a ranar Alhamis

Hukumomin kasar Pilipin sun ce sun dakatar da aikin ceto na sauran mutane 12 da suka bata a cikin hadarin jirgin ruwan da ya wakana, inda mutane 41 suka halaka. Sun ce sun dakatar da aikin ne sabili da rashin kyawan yanayi. A jiya Alhamis ne dai wani jirgin ruwan kasar ta Pilipin mai suna Le Kim Nirvana mai nauyin ton 33 mai yin jigilar fasinja a tsakanin wasu tsibiran kasar ya nutse yana dauke da mutane 189.

Mutane 134 ne dai masu ayyukan ceto suka samo da ransu. Sai dai ba a da duriyar wasu mutanan 12 wadanda hukumomin kasar suka dukufa neman su amma kuma aikin ya dakata sabili da rashin kyawun yanayi. Hukumomin kasar ta Pilipin sun ce kawo yanzu dai ba su da masaniya a game da abunda ya haddasa hadarin jirgin ruwan.