1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadaddiyar Daular Larabawa ta fice daga kungiyar OPEC

April 28, 2026

Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta dauki wannan matakin ne bayan yin dogon nazari kan muradunta na tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/5CyDd
Hadaddiyar Daular Larabawa ta fice daga kungiyar OPEC
Hadaddiyar Daular Larabawa ta fice daga kungiyar OPECHoto: Mohamed Messara/dpa/picture alliance

Sanarwar ficewar Hadaddiyar Daular Larabawa daga kungiyar OPEC ya yamutsa hazo, yayin da farashin makamashi ke ci gaba da tsada sakamkon rikicin yankin Gabas ta Tsakiya. Ana sa ran UAE da ke zama guda daga cikin kasashen duniya da suka fi samar da mai, za ta janye daga kungiyar a ranar Juma'a.

Karin bayani: Hadaddiyar Daular Larabawa na son ficewa daga Kungiyar OPEC

A cikin sanarwar da kasar ta fitar, ta ce matakin da aka dauka na da alaka da nazarin da aka yi na tsawon lokaci kan muradunta na tattalin arziki da kuma sauyin da aka samu a bangaren makamashinta. Ana dai ganin matakin zai raunata kungiyar, inda masu sharhi ke hasashen cewa hakan ka iya sa kungiyar ta fara tangal-tangal.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta kasance mamba a kungiyar tun a shekarar 1967.