Hada karfi wajen neman jirgin Malaysia | Labarai | DW | 16.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hada karfi wajen neman jirgin Malaysia

Kasashe 25 za su shiga aikin neman jirgin saman Malaysia da ya yi batan dabo a makon da ya gabata tsakanin biranen Kuala Lumpur da kuma Beijing na China.

Gwamnatin kasar Malaysiya ta bayyana a wannan lahadin cewa kasashe 25 ne ke cikin masu neman jirgin sama mallakin kasar, wanda ya bace kimanin kwanaki 10 da suka gabata dauke da mutane 239. An daina jin dauriyar jirgin ne jim kadan bayan da ya tashi daga Kuala Lumpur babban birnin kasar ta Malayisa a kan hanyarsa ta zuwa Beijing babban birnin kasar China.

Ministan kula da sufuri na kasar ta Malayisa Hishammuddin Hussein ya ce kasashen sun tashi daga 14 zuwa 25 saboda girman wuraren da za a gudanar da bincike. Rahotannin bincike na nuni da cewa jirgin ya yi tafiya mai tsawo kafin ya sauka ko ya fadi . Sannan babu wanda ya san mene ne ya faru. Yanzu haka abin da ake bincike shi ne gano inda jirgin ya shiga ko kuma baraguzansa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe