1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha za ta martaba sulhu da Eritrea

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 6, 2018

A wani mataki na sassauta halin fargaba da tashin hankali a tsakanin kasashen biyu Habasha da Eritrea za su martaba yarjejeniyar sulhu.

https://p.dw.com/p/2z2uF
Äthiopien Premierminister Dr. Abiy Ahmed
Sabon Firaministan Habasha Abiy AhmedHoto: Oromia Government Communication Affairs Bureau

Watanni biyu bayan darewa kan karagar mulki, sabon Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fara nuna azama ta kawo sauye-sauye da nufin bunkasa yanayin siyasar kasar. Batu na baya-bayan nan da Firaminsta Abiy ya bayyana shi ne na amfani da hukuncin kotun duniya da ke sasanta rikici tsakanin kasashe da ke birnin Hague na kasar Holand ta yanke a shekarar 2002 game da kan iyakar kasashen biyu, inda Eritrea da ke zaman abokiyar takun sakar Habashan da samu galaba. Shin ko sauye-sauyen da Abiy ya dauko za su yiwu? Tuni masana suka fara mayar da martani dangane da wannan mataki, Ludger Schadomsky shugaban sashen Amharik na tashar DW, ya yi tsokaci.

Einwohner Eritrea begrüßen Rückkehrer aus Äthiopien
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Nabil

"Wani tashe ne na fatan sauyi da ke zuciyar matashin Firaministan, wanda kuma ke da karfin fada aji a bangaren tsaro wanda har yanzu ke da karfi sosai, a yanzu dai sai mu zuba idanu muga ko zai iya aiwatar da dukkan sauye-sauyen da ya kudiri aniyar yi."

Sai dai ga Ulrich Delius daraktan wata kungiya mai rajin ganin Habashan ta girmama yarjejeniyar sulhun ya kuma ce matakin na Abiy na nufin samun karuwar zaman lafiya a yankin kahon Afirka, kana Abiy na kokarin cika alkawuran da ya dauka.

"A gaskiya, kawo yanzu ya aiwatar dukkan abin da ya ce zai yi, a dangane da haka babu wani dalili da zai sa a yi tunanin abin ba mai yiwuwa bane. Wannan mutumin ya san abin da yake yi kafin ma ya aiwatar, kuma zai yi bayani karara ga jami'an tsaro da sojojin kasar yadda za a yi amfani da yarjejeniyar."  

Eritrea Soldaten beim Training im Grenzkrieg mit Äthiopien 1999
Hoto: Getty Images/AFP/S. Forrest

Martin Plaut kwararre a kan kasar Habasha, ya nunar da cewa akwai matakin da ya kamata Majalaisar Dinkin Duniya ta dauka a nata bangaren idan har kasashen biyu suka tabbatar da amincewa da aiki da yarjejeniyar sulhun.

"Idan har aka tabbatar da cewa za a yi amfani da yarjejeniyar, to kuwa Majalisar Dinkin Duniya na da gagarumar rawar takawa domin ganin an kawo karshen takun sakar da ke tsakanin bangarorin biyu. Abin da ya kamaci al'ummar Eritrea a hukumance ko akasin haka shi ne, su rungumi batun sulhun, kasancewar al'ummar kasashen biyu na bukatar zaman lafiya. Rikicin ya dade sosai."

Matakin amfani da yarjejeniyar sulhun na Firaminista Abiy na kasar Habasha dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da jami'iyya mai mulki a nata bangaren ta sanar da cewa kasar da ke yankin gabashin Afirka, za ta bude kofofinta ga masu zuba jari da nufin sayar da hannayen jarin kamfanonin makamashi da na jiragen kasa da na sama da otel-otel da makamantansu.