1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha za ta yi wa Facebook kishiya

Abdul-raheem Hassan
August 23, 2021

Gwamnatin Habasha ta tabbatar da fara kirkiro manhajojin sadarwar zamani na kanta don yin gogayya da manyan kamafanonin duniya, sai dai hukumomin kasar sun ce ba su da niyyar rufe Facebook da twitter da Whatsapp.

https://p.dw.com/p/3zOV5
App Icons Facebook Whatsapp Snapchat Google Youtube Spotify
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Wolf

Wannan matakin na zuwa ne bayan cacar baka tsakanin gwamnatin kasar da kuma masu kishin yankin Tigray bayan barkewar rikici tsakanin sojoji da 'yan yankin. Gwamnati ta zargi Facebook da goge wasu shafuka da rubutu da ke bayyana hakikanin halin da kasar ke ciki a wancan lokaci.

Sai dai hukumomin kare hakkin dan Adam ta soki gwamnati da rufe wasu shafukan sada zumunta, ciki har da Facebook da Whatsapp da twitter a shekarun da suka gabata.