1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSomaliya

Somaliland: Fatan samun amincewar Habasha

May 13, 2024

Yankin Somaliland da ke da kwarya-kwaryar 'yanci daga Somaliya, na kokarin kammala wata yarjejeniya mai cike da rudani da makwabciyar kasa Habasha.

https://p.dw.com/p/4fnND
Habasha | Abiy Ahmed | Somaliland | Muse Bihi Abdi | Yarjejeniyar Fahimatr Juna
Firaministan Habasha Abiy Ahmed da shugaban kasar Somaliland Muse Bihi AbdiHoto: TIKSA NEGERI/REUTERS

In har suka kammala cimma wannan yarjejeniya dai, za ta sanya Addis Ababa ta amince da ita a matsayin kasa mai cikakken 'yanci duk da Somaliya na adawa da hakan. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da yankin na Somaliland ke shirin gudanar da bikin zagayowar ranar da ya samu 'yanci a ranar 18 ga watan Mayun 1991, koda yake har kawo yanzu al'ummomin kasa da kasa ba su amince da yankin a matsayin kasa mai cikakken 'yanci ba.

Karin Bayani: AU ta ja hankalin Habasha da Somaliya

Da zarar Addis Ababan ta amince da ita a matsayin kasa mai cikakken 'yanci, a nata bangaren Somaliland za ta bai wa Habashan damar amfani da ruwanta har tsawon kilomita 20 zuwa tsawon shekaru 50 tare da bai wa Habashan damar kafa sansanin sojojinta a gabar ruwan na Somaliland kamar yadda ministan harkokin kasashen ketare da dangantakar kasa da kasa na Somaliland din Essa Kayd ya bayar da tabbaci. Sai dai har a yanzu da al'ummar Somaliland din ke jin suna kara kusantar abin da suka kwashe tsawon lokaci suna mafarkin samu, mafarkin nasu na fuskantar gagarumar suka daga Somaliya.

Somaliland | Tashar Jiragen Ruwa | Berbera | Habasha | Yarjejeniya
Tashar jiragen ruwan Somaliland ta BarberaHoto: Eshete Bekele/DW

Somaliya dai ba ta taba amincewa da 'yancin kan da Somaliland ta ayyana samu ba, kuma Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya soke yarjejeniyar fahimtar junan da suka cimma bayan kwanaki biyar tare da zargin Habasha da kokarin mallake wani yanki na kasarsa Somaliya. Shugaban Somaliland din Muse Bihi Abdi ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a matsyin mataki na farko na cimma wannan yarjejeniya, tare da Firaminista Abiy Ahmed na Habasha. Koda yake ba a bayyana ciakken abin da ke yarjejeniyar da suka sanya hannu a kanta a watan Janairun wannan shekarar ta kunsa ba, mahukuntan Habashan sun ce za ta bai wa kasarsu damar kafa sansanin kasuwanci a tashar jiragen ruwan Somaliland din ta Berbera.

Karin Bayani: Tiruneh ya zama sabon mataimakin Firaiministan Habasha

Yankin Somaliland ya samu 'yancin cin gashin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a ranar 26 ga watan Yunin 1960, sai dai 'yancin na tsawon kwanaki biyar ne kacal. A ranar daya ga watan Yulin 1960 din, yankin na Somaliland ya hade da Somaliya wato Somali la Italiana da Italiya tai wa mulkin mallaka a baya tare da kafa kasar Jamhuriyar Somaliya da nufin hade kawunan masu magana da harshen Somali da Turawan mulkin mallaka suka kasafta a tsakaninsu.