1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin juyin mulki ya ci tuta a Habasha

Gazali Abdou Tasawa
June 23, 2019

Gwamantin kasar Habasha ta sanar da dakile wani yinkurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi jihar Amhara da ke a yankin Arewa maso yammacin kasar a jiya Asabar

https://p.dw.com/p/3Kvh0
Äthiopien Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Morrison

Gwamnatin kasar Habasha ta ce sojojinta sun yi nasarar dakile yunkurin da wasu sojojin kasar suka yi na kifar da gwamnatin Firamnistan Abiy Ahmed a jiya Asabar a jihar Amhara da ke a Arewa maso yammacin kasar inda babban hafsan sojojin kasar Janar Seare Mekonnen ya mutu bayan da sojojin suka harbe shi da bindiga. 

Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa firaministan kasar ta Habasha sanye da kakin soja ya fito a gidan talabijin na kasar inda tabbatar da yinkurin juyin mulkin da ma halaka babban hafsan sojan kasar. 

Ofishin jakadancin Amirka a birnin Adis Ababa ya gargadi ma'aikatansa da su buya bayan da aka samu labarin jin aman bindigogi a babban birnin kasar da ma a jihar ta Amhara da ke zama yankin na biyu wajen yawan al'umma a kasar. 

Hanyoyin sadarwar Intanet sun katse a kasar ta Habasha wanda ya sanya ba a da cikakkun labarai kan abin da ke wakana da kuma halin da ake ciki.