Habasha ta dauki matakan kawo karshen rikici da Iritiriya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 08.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Habasha ta dauki matakan kawo karshen rikici da Iritiriya

Taimakon raya kasa ga kasashen Afirka zai tabbata ne kawai idan an aiwatar da sauye-sauye domin hana karkata kudaden zuwa wasu hanyoyin da suka saba ka'ida.

Jaridar Der Spiegel ta ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta damu cewa shirin musamman na raya Afirka da aka yi wa lakabi da "Afirka Marshall Plan" da gwamnatinta ta bayyana ba ya tafiya cikin hanzari yadda ake bukata. Daga cikin manufofin shirin shi ne ba da rance ga wasu kasashe zababbu na Afirka domin tallafa musu da kudaden ayyukan raya kasa a fannin makamashi da muhalli.

Merkel ta sami koke daga Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana cewa har yanzu kasarsa ba ta ga ko da sisin kwabo ba saboda ma'aikatar kawancen tattalin arziki da raya kasashe ta Jamus ba ta mika musu jadawalin ka'idojin da ake bukata a cika kafin samun tallafin ba.

Ministan raya kasa Gerd Müller ya ce Ghana na bukatar aiwatar da wasu sauye-sauye tukunna kafin a tura mata kudin.

Jaridar ta ce an kammala duk tuntuba a tsakanin kasashen biyu, an kuma sanya hannu a kan yarjejeniya a karshen 2017.

Su kuwa jaridun Frankfurter Allgemeine Zeitung da Süddeutsche Zeitung sun yi sharhi kan wani mataki na ba zata da sabon Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya dauka na amincewa da hukuncin kotu kan takaddamar kan iyaka tsakanin Habashar da Iritiriya.

Tsawon shekaru kasashen biyu sun yi yaki da juna a 1998.

Einwohner Eritrea begrüßen Rückkehrer aus Äthiopien (picture-alliance/dpa/A. Nabil)

Iyakar Habasha da Iritiriya lokacin rikici tsakanin kasashen biyu a baya.

Jaridar ta ce wasu kasashe na yaki saboda mai ko wani arziki na albarkatun kasa, amma yaki tsakanin Habasha da Iritiriya yaki ne mara ma'ana domin yankin Badme da ke kan iyakar kasashensu wanda suke takaddama kansa ba yanki ne mai kunshe da wasu albarkatu ba. Mutane fiye dubu 100 suka rasu yayin da wasu kimanin miliyan daya suka yi kaura daga kasashen a lokacin yakin.

Kotun shari'ar iyakoki ta kasa da kasa ta mallaka wa Iritiriya yankin na Badme, to amma Habasha ba ta lamunta ba, tsawon shekaru 20.

Sai dai kwatsam ba zato ba tsammani sabon Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya sanar da cewa sun amince za su mika yankin gaa Iritiriya.

A yanzu dai a cewar jaridar babbar ayar tambaya ita ce shi ne ko shugaban Iritiriya Isayas Aferwerki zai karbi wannan tayi da hannu biyu-biyu? Tsawon shekaru 16 yana rokon kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya tilasta Habasha ta amince da hukuncin shari'ar kan iyakar ba tare da wata nasara ba, to yanzu ta fadi gasassa.

Jaridar Neues Deutschland ta rubuta sharhinta da taken "Magoya bayan tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na son wata sabuwar jam'iyya ta tagayyara ANC"

Jaridar ta ce jam'iyyar ANC wadda ke mulkin Afirka ta Kudu tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launinta a 1994 na fuskantar hali na gaba Kura baya Siyaki.

Südafrika Jacob Zuma (picture-alliance/dpa/EPA/A. Ufumeli)

Jacob Zuma tsohon shugaban Afirka ta Kudu

Magoya bayan Jacob Zuma suna barazanar ballewa domin kafa abin da suka kira ATC African Transformation Congress a Turance wadda za ta kunshi 'yan ra'ayin sauyi a cikin jam'iyyar da kuma gyauron 'ya'yan jam'iyyar ta ANC sannan da kungiyoyin addini.

Kawo yanzu dai Zuma bai fito fili ya goyi bayan wannan yunkuri ba, sannan kuma bai nesanata kansa daga yunkurin ba.