Habasha: Mata sun samu kashi 50 na mukamai
October 16, 2018Talla
Tun kafin mika bukatar sa ga zauren majalisar, sabon Firaministan mai shekaru 42 ya bayyana cewar yana fatan mata za su yi amfani da wannan tagomashi wajen nunawa al'ummar kasar cewar za su iya shugabanci fiye da maza. Daga cikin matan da aka nada a mukamansun hada da Aisha Muhammad Musa wacce ta samu mukamin ministar tsaro a karon farko a kasar.
Yanzu dai majalisar ministocin ta kunshi mutane 20 ne kachal maimakon 28 din da ta kasance a baya.