1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kiyaye dokokin kula da fursunoni a Habasha

Salissou Boukari
July 5, 2018

A wannan Alhamis din ne gwamnatin Habasha ta kori wasu manyan jami'an kula da wani gidan yari 'yan sa'o'i gabannin kungiyar kare hakkin bil'adama ta HRW ta saki rahoton zargin muzguna wa fursunoni.

https://p.dw.com/p/30uVf
Brasilien Gefängnisinsassen üben Yoga nach dem Besuch der Familie
Hoto: Reuters/N. Doce

Tuni dai bayan koran mutanen gwamnatin kasar Habasha ta kuma maye gurbi jami'an da aka kora bisa laifukan take doka da oda wajen muzgunawa fursunonin da ke tsare a kurkuru, sai dai Atoni janar na kasar ya kirayi sabbin jami'an da aka nada da su mutunta hakkin dan adam wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Cikin sabon rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adaman ta fitar, kan yadda fursunoni ke shan duka da tozartawa daga jami'an da ke kula da tsaron su a gidan yarin, rahoton ya ce shekaru da dama ba a kula da lafiyar fursunoni yadda ta kamata. Wani firsina da ya bada labarin yadda ake gallaza musu azaba ya ce: " 'Yan sanda da masu tsaron gidan yarin na jera fursinonin ne, su cire musu kaya ana gallaza musu azaba da duka da sanduna. Haka suke sa su kwanciya a kasa suna bi ta kansu suna taka su".

Shi kuma wani firsina mai suna Hodan, cewa ya yi: "Za a kaika cikin kurgumin duhu kuma a tilasta maka cewa kana kaunar su, har idan ka ki fadi hanayenka biyu da kafafuwa za'a daure har sai itatuwan wuta da aka kunna sun koma rushin wuta  sai a sa ka kwanta a kai. Don a tsorata mutum ya fadi abin da suke su ji."

Felix Horne na daya daga cikin  wadanda suka gudanar dan wannan  bincike na halin da fursinoni ke ciki a gidajen yarin kasar Habasha, ya zargi gwamnatin baya da nuna halin ko in kula dangane halin rayuwar firsinonin. Amman yanzu da zuwan wannan sabuwar gwamnatin akwai fatar lamura zasu sauya.