Habasha: Cibiyar Gahawa
Bonga gari ne da ke kudu maso yammacin kasar Habasha, nan ne ake samun gahawar nan ta Arabica coffee ko da dai wajen bai yi fice ba sosai. A wannan gari ne aka gano gahawa shekaru da dama da suka gabata.
Bakin Zinare
Yawan Gahawa ko coffee din da aka noma tsakanin bara da wannan da shekarar zai iya kaiwa buhuna miliyan 143 million. Wannan ne ma ya sanya shi zama abu na biyu da aka fi kasuwancinsa a duniya bayan man fetur. Ana batar da miliyoyin daloli wajen cinikinsa kuma kasuwancinsa ya samo asali ne daga garin Bonga na kudancin kasar Habasha.
Inda aka fara noman Gahawa
Duk da cewar a Bonga aka fara noman Gahawar da aka fi sani da suna Arabica coffee, da wuya ka ji an ambaci sunan garin. Kamfanoni na kallon garin a halin yanzu a matsayin wajen da ke samar da Gahawa din da bai taka kara ya karya ba. Bonga dai na da girman murabba'in kilomita 500 kuma waje ne mai dazuka da ke da bishiyoyi na Gahawa da yawa kana ana samun zuma a wajen.
Makiyayi mai son ganin kwakwaf
An nunar da cewar wani makiyayi mai suna Kaldi ya hangi awakinsa na cin wani dan itace ja da bai taba gani ba, da ya lura abin ya yi wa dabbobin dadi sai shi ma ya yanke shawarar dandanawa. Daga nan ne ya gano kwayoyin da ake kira Coffee ko Gahawa. Ita dai kalmar ta samo asalinta ne daga Kaffa, wanda tsohon suna ne na lardin nan na Oromia wanda garin Bonga ke karkashinsa.
Amfani da takin gargajiya
Mafi yawan masu noman Gahawa a Habasha kananan manoma ne. Sakamakon karancin kudi na sayen takin zamani, manoman na amfani da takin gargajiya wajen noma shi wanda hakan ya sanya Gahawar ke da kyau matuka. Habasha ce ke kan gaba wajen noman Gahawa a duniya kuma kimanin mutane miliyan 15 ne ke cin abinci da wannan sana'a ta noman Gahawa a kasar.
Masana'antar Gahawa ta asali
Yanayin wannan dajin alama ce da ke nuna kyawun da Gahawar da ake nomawa a Habasha ke da shi. Inuwar da bishiyoyi a dajin ke samarwa na sanya Gahawar girma sannu a hankali wanda hakan kan sa dandanonsa ya yi dadi sosai. Bishiyoyin Gahawa ko Coffee ba su cika yin tsawo ba don haka za a iya cirar 'ya'yan cikin sauki.
Bishiyoyi masu zaki
Irin furannin da ke dazukan Habasha na sanya yawaitar kudan zuma. Manoma kan yi kokari wajen ganin kudajen na zuma sun kasance a wuraren da suke don samar da zuma.Wannan yunkuri nasu na aiki domin duk inda ka duba a Bonga zuma za ka gani iri daban-daban. Ana amfani da galibin zumar da ake samu wajen yin wata barasa ta musamman da ake kira 'tej.'
'Ya'yan itace
"Bazan iya kaura zuwa birni in bar wannan ba", inji wani mai kiwon zuma da ake kira Mirutse Habtemari. A hirarsa da DW Mirutse ya nuna irin albarkatun da ke kauyensu wanda suka hada da kayan lambu kamar ayaba da koren tattasai da furanni da makamantansu.
Jebena bunna: Tukunyar dafa Gahawa
Daga cikin abubuwa masu muhimmanci a wannan kauyen har da al'adar nan ta bikin shan Gahawa da ake da ita a Habasha. A kan gasa danyun kwayoyin gahawa a kan gawayi sannan a dake su cikin turmi kafin a dafa a tukwanen kasa da ake kira 'jebena.' Wannan ita ce hanya mafi kyau ta samar da Gahawa wadda ake kira 'bunna' a harsuna da dama na Habasha.
Babu Gahawa mai daci a nan
Sakamakon irin yanayin da ake noman Gahawa a Habasha, abu ne mai wuya a samu Gahawa da ke da daci. Galibi ta kan kasance mai zakin gashe da dandano iri daban-daban. Bisa ga irin kididdigar da aka yi, Habasha na da nau'in Gahawa kusan kala dubu shidda.
Kyauta ga duniya
A bara firaministan Habasha Hailemariam Desalegn ya ziyarci Bonga don kaddamar da wani gidan adana kayan tarihi na Gahawa a kasar. Wannan dai na daga cikin yunkurin da akeyi na fito da sunan Bonga a duniya. A hannu guda kuma masana'antar Gahawa ta kasar na kokari wajen gogayya da takwarorinta na duniya ta fuskar cinikayya domin amfana da wannan arziki da Habasha ke da shi tun kaka da kakkani.