Habaka tattalin arzikin Afirka da na Larabawa | Labarai | DW | 19.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Habaka tattalin arzikin Afirka da na Larabawa

Afirka da kasashen Larabawa za su daddale hanyoyin karfafa huldar tattalin arziki a tsakaninsu.

A wannan Talatar (19. 11. 13) ce kasashen Afirka da na Larabawa ke bude taron koli na yini biyu a kasar Kuwait domin bitar matakan da suka dauka na karfafa huldar tattalin arziki a tsakanin kasashen yankin tekun Fasha da ke da karfin tattalin arziki da kuma zuba jarinsu a nahiyar ta Afirka. Wannan taron dai shi ne zai kasance mafi girma irinsa na farko tun bayan wanda ya gudana a shekara ta 2010, yayin da shugabannin sassan biyu suka gana a kasar Libiya, gabannin juyin juya halin kasashen Larabawa, wanda yayi awon gaba da mai masaukin bakinsu a wancan lokacin, wato marigayi shugaba Ghaddafi da kuma wasu takwarorinsa a wasu kasashen arewacin Afirka da kuma na yankin Gabas Ta Tsakiya. Ana dai sa ran shugabannin kasashe 23 da kuma mataimakan shugabanni bakwai, game da shugabannin gwamnatoci uku ne za su halarci taron kolin, wanda ke da nufin karfafa harkokin tattalin arziki a tsakanin yankunan biyu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu