Gwatamala : za a cire rigar kariyar shugaban kasa | Labarai | DW | 01.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwatamala : za a cire rigar kariyar shugaban kasa

Majalissar dokokin kasar za ta kada kuri'ar neman cire rigar kariyar Shugaba Otto Perez wanda ake zargi da cin hanci a kasar.

A kasar Gwatamala a wannan Talata ce majalissar dokokin kasar ke gudanar da mahawarar neman cire rigar kariya ga Shugaban Kasar Otto Perez wanda ake zargi da aikata cin hanci a kasar.Wannan ya zo ne kwanaki ukku bayan da wani komitin bincike da majalissar dokokin kasar ta kafa ya bada shawarar cire wa shugaban wanda dama ke fuskantar zanga-zangar nuna adawa da milkinsa daga al'ummar kasar rigar kariyarsa.

Matakin cire rigar kariyar shugaban kasar zai tabbata ne idan aka samu kuri'u 105 daga cikin 158 a kuri'ar da 'yan majalissar dokokin kasar za su kada a karshen mahawarar da za su tabka kan batun a wannan rana ta Talata. Idan dai har hakan ta tabbata to kwa wannan zai zama karo na farko da wani shugaban kasar ta Gwatamala zai rasa rigar kariyarsa a tarihin kasar.