Gwarzayen Jama′a: Godiya da gudunmawarku | Zamantakewa | DW | 24.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gwarzayen Jama'a: Godiya da gudunmawarku

An kawo karshen karbar labaran wadanda suka shiga gasar Gwarzayen Jama'a na DW.

Wa'adin turo da ra'ayoyi game da mutanen da ke zama gwarzayen jama'a a yankunanku ya kawo karshe, amma gwarzayen jama'a na DW za su ci gaba. A tsawon watan da ya gabata mun samu labarai game da gwarzayen jama'a daga ko ina cikin duniya. Wadannan labarai sun taimaka sun kuma ba da bayanai game da mutanen da ke taka muhimmiyar rawa don kawo sauyi mai ma'ana a yankunansu ko kuma cikin al'ummarsu.

Godiya ga dukkan wadanda suka ba da gudunmawa. Za mu yi nazarin dukkan labaran da muka samu sannan mu zabi wadanda suka yi nasara a cikin makonni masu zuwa.

Kafin lokacin sai ku ci gaba da sanya ido a shafinmu na intanet wato: #link:http://dw.com/localheroes# inda za mu sanar da ku wadanda suka yi nasara, ko kuma ku kasance da mu a shirye-shiryen telibijin na DW don samun labaran wasu gwarzayen jama'a da sauran mutanen da ke taka rawa wajen inganta rayuwa a duniya.

Akwai karin bayani kan gwarzayen jama’a na DW a sabuwar tasharmu ta Turanci a #link:http://dw.com/localheroes#

Kyaututtuka
- Na farko: Na’urar „tablet" da wasu karin kyaututtuka
- Na biyu da na uku : Na’urar sauraron sauti ta Ipod da wasu karin kyaututtuka
- Kyauta ta karfafa gwiwa : kyauta daya daga cikin bakwan da aka tanadar wa gwarzayen jama‘a

Karin shafuna a WWW