Gwamnatin Tunisiya za ta yi garambawul ga tattalin arziki
March 23, 2018Talla
Firaminista Youssef Chahed na kasar Tunisiya ya jaddada shirin gwamnatin kasar na sake fasalin kamfanonin gwamnatin cikin hanzari domin zaburar da tattalin arzikin kasar da ke yankin arewacin Afirka, wanda ke cikin mawuyacin hali gami da fama da gibin kasafin kudi.
Kungiyoyin kwadago sun nuna tirjiya bisa matakan da gwamnatin ke dauka saboda rasa guraben aiki da zabtare kudaden jin dadin mutane. An dade ana nuna adawa da matakin gwamnati na Tunisiya kan cefanar da kaddarorin gwamnati ga 'yan kasuwa, domin garambawul ga tattalin arziki kasar.