Gwamnatin Thailand ta neman wadanda suka kitsa kai hari | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Thailand ta neman wadanda suka kitsa kai hari

An tabbatar da mutuwar fiye da mutane 20 sakamakon bashewar bam da aka samu a birnin Bangkok fadar gwamnatin kasar

An tabbatar da mutuwar fiye da mutane 20, yayin da wasu mutane fiye da 100 suka samu raunika, lamarin da ke neman kassara yawon bude ido na kasar.

Kusan kashi 20 cikin 100 na kudaden shigar kasar yana fitowa daga wajen yawon bude ido, kuma duk rikice-rikice da ake samu na siyasa a kasar ba su yi tasiri ba kan wannan fannni, amma masana sun nuna cewa hari kamar wanda aka sama a wannan Litinin da ta gabata zai yi mummunan tasiri kan yadda baki suke ziyarar kasar. Tun shekara ta 2006 kasar take fuskantar rikice-rikicen siyasa da juye-juyen mulki na soja.

Gwamnatin kasar ta Thailand ta ce tana bin sawun duk yadda za ta kama wadanda suka kitsa harin. Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.