Gwamnatin ta yi murabus a Palasdinu. | Labarai | DW | 29.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin ta yi murabus a Palasdinu.

A Palasdinu Firaministan Rami Hamdallah da majalisar ministocinsa sun yi murabus a wannan Talata.

Kamfanin dillancin labaran Palasdinu na Wafa ne ya wallafa wannan labarin, ina da ya ce tuni Shugaba Mahmud Abbas ya karbi takardar murabus din wanda a ke dangantawa da sabanin da ake ci gaba da samu tsakanin Kungiyoyin Palasdinawa na Fatah da kuma Hamas. 

Sai dai Shugaba Abbas ya bai wa gwamantin mai murabus damar ci gaba da gudanar da al'amura a matsayin na wucin gadi kafin kai ga samar da wata sabuwar gwamnati.

Masu sharhi kan harkokin siyasar Palasdinu dai na fassara matakin na Shugaba Abbas da wani yunkuri na neman kafa sabon kawance da zai bashi damar rage karfin kungiyar Hamas da ke rike da iko a zirin Gaza .

Sabanin da ke da tsakanin kungiyoyin na Palasdinawa dai na a matsayin dalilin kasa shawo kan rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin Palsdinawa da Isra'ila na samar da kasashE biyu MASU makwabtan juna.