Gwamnatin Nasarawa ta fara tsugunar da yan gudun hijira | Zamantakewa | DW | 30.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gwamnatin Nasarawa ta fara tsugunar da yan gudun hijira

Gwamantin jihar Nasarawa tace za ta yi kokarin ganin dukkan mutane da suka gujewa garuruwan su sanadiyyar rikicin kabilanci a jihar sun koma garuruwan su na asali.

Religiös motivierte Unruhen in Zentralnigeria Photograph made available 25 January 2010 shows a Nigerian women walking past soldiers patrolling in the Nigerian city of Jos following a week of religious violence in the central Plateau district, Nigeria 22 January 2010. Fighting between gangs of Christian and Muslim youths claimed more than 300 lives with millions of Naira worth of properties destroyed and hundreds of people displaced. EPA/GEORGE ESIRI +++(c) dpa - Bildfunk+++

Religiös motivierte Unruhen in Zentralnigeria

Ya zuwa yanzu ma har gwamnatin ta samar da kwanukan rufin gidaje da buhunan siminti tare da tsabar kudi ga wadanda suka gujewa tashin hankalin garin Assakio.

Jihar Nassarawa dai ta shiga kanun labarai a 'yan watannin baya sakamakon yawan tashe tashen hankula na kabilanci, lamarin daya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyin jama'a da dama. Yanzu haka dai dubban jama'a mazauna garuruwan Obi, Assakio da wasu kauyuka da dama sun gujewa garuruwan su na asali sakamakon tashin hankalin daya auku tsakanin kabilun Eggon da Alago.

Kasancewar yanzu gwamnatin tarayya ta tura jami'an tsaro zuwa wuraren da aka yi tarzomar, gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki matakan ganin mazauna kauyukan sun koma garuruwa da suka baro, inda ta tura tireloli dauke da buhunan siminti, da kwanukan rufi da kuma tsabar kudi naira milyan 45 ga mazauna Assakio don su soma aikin gini. Ko yaya jama'ar kauyen ke ganin matakin haka. Wasu da suka zanta da radiyon D W sun bayyana gamsuwa da jin dadi sabili da samun taimakon, kana sunce zasu koma muddin suka samu taimakon gwamnati.

To sai dai kuma yan kabilar Eggon sun soma korafi cewar ba'a rabon irin wannan kayayaki dasu, kasancewar hukumomin jihar na zargin yan kabilar ce da laifin tada tarzoma a jihar kamar yadda kakakin yan kabilar Eggon dake Assakio ya shaida mini. Wannan lamari na rikicin kabilancin jihar Nasarawa dai ya zamanto abin damuwa, inda akasari mazauna kauyuka da abin ya shafa suka tarwatse zuwa wasu garuruwa dake jihohi makwabtan Nasarawa, inda wasu 'yan jihar dake neman mafaka a garin Namu cikin jihar Filato suka kamu da ciwon amai da gudawa. To me gwamnatin jihar keyi don ganin al'ummar da suka gujewa taromar sun koma cikin gaugauwan? Gwamna Tanko Almakura shine gwamnan jihar Nasarawa, ya amsa wannan tambaya.

Yace sun rigaya sun hada guiwa da gwamnatin tarayya don samar da cikkaken tsaro da kuma tallafin da zai bada zarafi ga jama'ar yankunan da abin ya shafa su koma garuruwan su na hasali.

To a halin yanzu dai gwamnatin jihar tace zata ci gaba da samar da kudi da kayan gini ga jama'a domin su sami zarafin komawa dukkanin garuruwa da suka baro su sanadiyyar wannan rikici na kabilanci.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita: Umaru Aliyu