1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta nada alkalan kotun tsarin mulki

August 11, 2020

Byan fama da jerin zanga-zanga da boren kyamar gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita, kasar Mali ta rantsar da sabbin alkalan kotun tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/3glrH
Mali | Präsident Ibrahim Boubacar Keita
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Nadin da aka yi wa sabbin alkalan kotun tsarin mulkin ya zo bayan shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da ake wa lakabi da IBK, ya rusa kotun tsarin mulkin kasar a sakamakon tirjiyar da masu zanga-zanga da gwamnatinsa suka nuna a kan kotun.

Sabbin alkalan su tara sun sha alwashin jagorantar bangaren shari'a na kasar cikin adalci ga kowane bangare kamar yadda babban jojin kasar Amadou Ousmane Touré ya yi alkawari.


Rantsar da sabbin alkalan kotun tsarin mulkin ta Mali na zuwa ne a yayin da a wannan Talata kungiyar nan ta M5 wacce ke adawa da gwamnatin Shugaba IBK ta shirya ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnati.