Gwamnatin Mali ta kulla yarjejeniya da ′yan tawaye | Labarai | DW | 24.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Mali ta kulla yarjejeniya da 'yan tawaye

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi nasarar shawo kan rikicin Mali bayan da ta kai bangarorin biyu da ke takaddama da juna kan teburin tattaunawa har suka kulla yarjejeniya

Gwamnatin Mali da kungiyoyin 'yan tawayen nan uku da suka gama kai suka karbe iko daga garin Kidal a yankin arewacin kasar, sun sanya hannu kan wata yajejeniya ta zaman lafiya da nufin kawo karshen dauki ba dadin da su ke yi.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU kana shugaban Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ne dai ya shiga tsakani wajen sasanta gwamnatin Malin da 'yan tawayen, a wata ziyara da ya kai kasar tun jiya Juma'a, wadda hakan ne ya taimaka wajen sanya hannu kan yarjejeniyar.

Da ya ke maida martani kan wannan cigaban da aka samu, shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita ya ce ya ji dadin irin kokarin da shugaba Ould Abdel Aziz ya yi, wanda ya nunawa 'yan tawaye cewar babu wani abu da ya fi zaman lafiya muhimmanci.

Gabannin kaiwa ga wannan gabar dai, rikicin tsakanin gwamnati da na 'yan tawayen ya yi sanadiyyar rasuwar sojin Mali 20 tare da jikkata wasu sama da 30.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu Waba