Gwamnatin Kwango ta yi ahuwa ga 'yan tawayen M23
September 3, 2014Talla
Kakakin gwamnatin na Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango Lambert Mende wanda ya bayyana sunayen tsofin 'yan tawayen da gwamnatin ta yi wa ahuwa.
A lokacin wani taron manema labarai ya ce sun yi hakka ne ga waɗanda suka buƙaci a yi musu ahuwar. Gwamnatin ta Kwango ta ce kusan kishi 80 cikin ɗari na bradan tsohuwar kungiyar 'yan tawayen suna a ƙasar Yuganda yayin da ake tsare da wasu a gidajen kurku na garin goma da ke a yankin arewa maso gabashin Kivu
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman