Heiko Mass zai je Tsibirin Madeira
April 18, 2019Talla
Helge Braun darakta a fadar gwamnatin ta Angela Merkel ya ce ministan na harkokin waje na Jamus Heiko Maas zai je tsibirin na Madeira domin ganin halin da ake ciKI. Zai kuma tafi ne tare a rakiyar likitoci domin ba da kulawa ta musammun ta kiwon lafiya ga wadanda suka raunana a sakamakon hadarin. Motar bas din wacce ke dauke da Jamusawa 49 maza da mata 'yan yawan shekatawa masu shekaru 40 zuwa 60 ta kife da su bayan da matukin motar ya saki daben da yake kansa.