1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha da Eritiriya sun rungumi tsarin zaman lafiya

Ramatu Garba Baba
June 6, 2018

Gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed ta kasar Habasha, ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a birnin Algiers a shekarar 2000 domin kawo karshen yaki da kasar Eritiriya.

https://p.dw.com/p/2yzwu
Eritrea Bevölkerung feiert Referendum 1993
Hoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Hakan yana nufin kasar Habasha za ta fice daga cikin wuraren da ake tababa kimanin shekaru 20 da suka gabata. Zuwa yanzu gwamnatin Eritiriya ba ta bayyana matsayinta kan matakin da makwabciyarta ta daukaba.

Kana gwamnatin ta Habasha ta amince da kawo karshen aiki da dokar ta baci da aka sanya a kasar watanni biyu da suka gabata. Tun lokacin da ya dare madafun iko Firaminista Abiy Ahmed ya soma daukan matakan inganta matsayin kasar tsakanin kasashen duniya, ya kuma yadda da bude kofar kasar ga harkokin kasuwanci domin 'yan kasuwa na kasashen ketere su zuba jari a wuraren da aka mamaye da harkokin gwamnati.