Gwamnatin Ghana ta dakarar da wasu alkalai | Labarai | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Ghana ta dakarar da wasu alkalai

Alkalai bakwai daga cikin 12 da ake binicke aka dakatar bayan bankado badakalar cin hanci da rashawa da wani dan jarida mai binciken ya yi.

Gwamnatin kasar Ghana ta dakatar da alkalai bakwai daga cikin 12 wadanda ake bincike bisa zargin cin hanci da rashawa da wani dan jarida ya bankado. A cikin wata sanarwa hukumar sharia ta kasar ta ce mataimakin shugaban kasar Kwesi Bekoe Amissah-Arthur wanda yake aiki a madadin Shugaba John Dramani Mahama da ke ziyara a Faransa, ya amince da matakin.

Kasar ta Ghana da ke yankin yammacin Afirka tana cikin wadanda suke samun kyautatuwar demokaradiyya.