1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Shugaban Amirka ya kare matakin janye dakaru a Afghanistan

Suleiman Babayo ATB
August 17, 2021

Shugaban Joe Biden na Amirka ya ce gaskiyar ita ce lamura sun sukurkuce cikin kankanin lokaci a Afghasnitan fiye da yadda ake tunani saboda sojojin kasar ta Afghanistan sun gaza yin fada domin kare kasarsu.

https://p.dw.com/p/3z4Fg
Washington Rede Präsident Biden Aghanistan
Hoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Shugaba Joe Biden na Amirka ya yi barazanar daukan tsauraran matakan kan 'yan Taliban da suka kwace madafun ikon kasar Afghanistan muddun suka kai hari kan Amirkawa yayin da sojojin Amirka ke ci gaba da aikin kwashe da 'yan kasashen ketere. Sannan shugaban ya kare matakin janye sojojin Amirka daga Afghansitan da ya janyo rudani.

Shugaban Biden ya daura alhakin abin da ya faru na sukurkucewar lamura kan shugabannin Afghansitan da suke tsere daga kasar da sojojin Afghansitan da suka gaza yaki.

Gwamnatin Amirka ta ware makuden kudade wajen sake tsugunar da 'yan Afghanistan da suka taimaki Amirka domin ficewa da sake gina rayuwa a kasashen ketere.