Gwamnatin ƙasar Masar na fuskantar ƙalubale | Labarai | DW | 27.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin ƙasar Masar na fuskantar ƙalubale

Ƙungiyoyin 'yan addawa sun dage sai shugaba Mohamed Mursi ya yi watsi da wata ayar doka, mai ba shi cikkaken iko

Gomai na duban jama'a sun yi cikkar kwari a dandali Tahrir na birnin Alƙahira na ƙasar Masar a rana ta biyar jere; na gangamin nuna rashin amincewa da wata ayar doka da gwamnatin shugaba Mohamed Mursi ta amince da i'ta.

Gangamin wanda ƙungiyar 'yan addawa ta ƙasar ta tsara na buƙatar gwamnatin ta Mursi da ta soke ayar dokar, wacce ta ce za ta sake saka ƙasar cikin wani hali na mulkin kama karya.'Yan sanda sun riƙa yin amfani da barkwano tsohuwa akan masu yin zanga zangar ,waɗanda shugabanin ƙungiyar suka gargaɗe su da su kaucewa yin fito na fito dasu.Tun lokacin da aka fara yin yamutsin dai a ranar Alhamis da ta gabata mutun ɗaya ya mutu yayin da wasu sama da ɗari ukku suka jikata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu