Gwamnati na ciyar da jama′a lokacin azumi | Zamantakewa | DW | 02.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gwamnati na ciyar da jama'a lokacin azumi

Gwamnatocin jihohi a Tarayyar Najeriya kan ɗauki nauyin ciyar da jama’a a lokacin azumin watan Ramadan, sai dai ra'ayoyin al'umma ya ban-banta kan wannan shiri.

Kimanin Naira miliyan 45 ne dai gwamnatin jihar Nija ta ware domin ciyar da marasa ƙarfi da abincin buɗe baki a lokacin azumin bana a masallatai da cibiyoyin 25 da aka ware a fadin jihar. Ɗaukan wannan mataki na ciyar da marasa ƙarfi kamar yadda gwamnatin ta ce zai taimaka wajen rage raɗadin talauci ga marasa ƙarfi a wannan wata na azumin Ramadan.

Gwamnatin na rarraba abincin ga jama'a a unguwani daban-daban

Jemen Al Saleh Moschee

Masallatai a nan ne galibi jama'a ke taruwa domin buɗa baki

Masallacin Juma'a na Shekh Nafiu Sauka ka huta Minna na ɗaya daga cikin masallatan da ake ciyar da mabuƙatan kamar yadda Malam Muhammad Mustafa Abdullahi ya shaidar. Sai dai kuma duk da wannan ƙoƙari na gwamnatin wasu mabukatan sunce sukan ba su gani a ƙasa ba a yayin da wasu kuma ke cewa ba su gamsu da yadda gwamnatin ke gudanar da shirin rabon abin buɗe bakin ba.

Matasa sun fi kowa cin gajiyar shirin

Nigeria Ramadan Fastenbrechen in Sokoto

Wasu mutane da suka karɓi abincin buɗa baki a Najeriya.

Matasa dai na ɗaya daga cikin rukunin jama'ar da wannan shiri na ciyar da marasa galihu a lokacin azumin ya shafa don haka na tambayi kwamishinan harkokin Matasa na jihar Nija Alhaji Muhammad Garba abin da ya yi ƙarin haske game da ƙorafe- korafen jama'a kan wannan shiri na gwamnatin jihar

Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar