Gwamnati da ′yan tawaye na Sudan ta Kudu na tattaunawa | Labarai | DW | 04.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnati da 'yan tawaye na Sudan ta Kudu na tattaunawa

Rahotannin daga Addis Abbaba na cewar an sake komawa kan tebrin shawarwari tsakanmin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar.

Hukumar IGAD ta ƙasashen gabashin Afirka wacce ke shiga tsakanin ta gargaɗi shugabannin biyu da cewar, za a samesu da laifin ci gaban faɗan. Idan a wannan karon ba su samu masalha ba, don kafa gwamnatin haɗaka ta riƙon ƙwarya kafin nan da ƙarshen wannan wata.

A cikin watan Yuni da ya gabata ne shawarwari tsakanin Salva Kiir ɗin da tsohon mataimakinsa suka cije wanda suka riƙa zargin junansu da kawo tarnaƙi. Kawo yanzu dubban jama'a suka rasa rayukansu a tsahin hankali wanda ya tilasta wa mutane sama da milyan ɗaya da rabi tsrewa daga matsugunansu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe