Gwajin kwakwalwa ga maharin Christchurch
April 5, 2019Talla
A wani zama da kotun ta yi a wannan Juma'ar, mai shari'a Cameron Mander ya ce wasu kwararru za su duba kana su tantance ko Brenton Tarrant na da cikakken hankalin da zai iya fuskantar shari'a.
Yayin zaman kotun na yau, Brenton mai shekaru 28 da haihuwa, wanda dan asalin kasar Austreliya ne ya gurfana gaban alkalin ne ta faifan bidiyon da aka haska kai tsaye daga gidan yarin da ake tsare da shi a birnin Auckland.
Mutanen da suka jikkata da kuma 'yan uwan wadanda suka rasu a harin na 15 ga watan Maris da dama ne dai suka halarci zaman kotun a birnin na Christchurch.