Gwagwarmayar gamayyar ƙasa da ƙasa wajen yaƙi da yaɗuwar AIDS | Siyasa | DW | 30.11.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gwagwarmayar gamayyar ƙasa da ƙasa wajen yaƙi da yaɗuwar AIDS

Daya ga watan Disemba rana ce ta mussamman a faɗin duniya wajen faɗakarwa game da cutar AIDS.

Daya ga watan Disemba,na ko wace shekara rana ce wadda Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe don yaƙi da yaɗuwar cutar AIDS.Kasar Nijar kamar sauran ƙasashen Afirka ana fama da wannan cutar.

Albarkacin zagayowar wannan ranar hukumomin Nijar tare da ƙungiyin masu hannu da shuni da ke yaƙi da yaɗuwar cutar Sida sun ware mako guda, domin matsa ƙaimi ga kanfen ɗin makon faɗakarwa.Uwagidan shugaban kasa,Madam Isufu Hajiya Aisata ke uwa ga hukumar yaƙi da cutar AIDS a Niger,ta jagoranci waɗannan shagulgulan.

Gwamnatrin Nijar tare da taimakon ƙungiyoyi masu hannu da shuni sun yi rawar gani rwajen rage yaɗuwar AIDS a ƙasar.

Dokta Fatuma itace shugabar ku a da masu cutar Sida a birnin Yamai ,tace duk da ƙoƙarin murƙushe wannan cuta ko wace rana suna samun mutanwe 15 zuwa 20 sabun kamu.Daga buɗe cibiyar kulla da masu Sida a birnin Yamai zuwa yanzu sun samu mutane aƙalla 4.400 masu ɗauke da ƙwayoyin cutar.

Daga cikin su akwai kusan dubu biyu masu karɓar magani a wannan cibiya.Amma matsalar da ake fama ita, ita ce adawar da mutane ke nunawa ta auna jininsu domin a haƙiƙance matsayin su game da cutar AIDS.

Masu fama da cutar AIDS sun kafa ƙungiya wadda ke kula da tattalin da ake masu.

Abubakar Sidiku Alhusaini Maiga ,shine shugaban ƙungiyar, kuma ya shaidi cewar ana kula da su bakin gwargwado kuma ana basu magani kyauta ruwan Allah.

A nasu waje, ƙungiyoyi masu zaman kansu kamar su Anima Sutura suna taka rawar gani wajen yaƙi da cutar Sida .Shugaban wannan ƙungiya ya ce suna aiki tare da direbobi a tashoshi fiye da 20 da kuma sojoji a cibiyar Soja ta Tondibiya da sauran masu kayan sarki.

Banda aiyukan faɗakarwa akwai tallafi na mussamman da ake baiwa mata masu ɗauke da cutar Sida domin girka sana'o'i.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita:Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 30.11.2012
 • Muhimman kalmomi Sida
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16tpU
 • Kwanan wata 30.11.2012
 • Muhimman kalmomi Sida
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16tpU