1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Ba za mu shiga rikicin Venezuela ba

Abdul-raheem Hassan
February 5, 2019

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ba zai shiga yunkurin da wasu kasashe ke yi na warware tambarwar siyasar kasar Venezuela ba.

https://p.dw.com/p/3CifR
UN-Klimakonferenz 2018 in Katowice, Polen | Antonio Guterres, UN-Generalsekretär
Hoto: Getty Images/AFP/J. Skarzynski

Kasashen Mexico da Yurugai na shirin hada kan kasashen duniya tare da Majalisar Dininkin Duniya zuwa babban taro a Montevideo babban birnin kasar Yurugai a ranar Alhamis domin samar da mafita kan rikicin siyasar da ya barke a Venezuela. Rikicin shugabanci a Venezuelan dai ya raba kan kasashen duniya, inda kasahsen Amirka, Faransa da Jamus da Spain da Kanada da kuma Ostireliya ke nuna goyon bayansu ga jagoran adawa Juan Guido, yayin da Rasha da China ke tsayin daka ga Shugaba Nicolas Maduro.