Gurfanar Morsi a gaban kotun Masar
November 4, 2013Talla
An ba da rahoton cewar an kashe wasu 'yan sanda guda biyu a kusa da birnin Isma'iliya na ƙasar ta Masar lokaci kaɗan kafin a soma gudanar da shari'ar tsohon shugaba Morsi tare da wasu 'yan Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulumi guda 14. Ana tuhumar Morsi da tunzura jama'a wajen haddasa yamutsin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama watannin da suka gabata.
An baza 'yan sanda kusan dubu 20 domin fuskantar zanga-zangar da Ƙungiyar ta 'Yan Uwa Musulumi ta yi kira. Yanzu haka kuma gidan telebijan na ƙasar ta Masar ya ce an iso da tsohon shugaban daga wani wurin sirrin da ake tsare da shi, zuwa wata cibiyar 'yan sanda inda za a fara yi masa shari'a.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe