Gurɓacewar muhalli a kudancin Najeriya | Labarai | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gurɓacewar muhalli a kudancin Najeriya

Ƙungiyar kare hakin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana fargabanta dangane da ƙaruwar barazanar da muhali ke fuskanta a Najeriyar.

Ƙungiyar ta Amnesty ta yi kashedi dangane da bazarnar ƙara samun gurɓacewar muhali a kudancin Najeriyar a sanadiyyar malallar ɗanyan man fetur.Hakan kuwa ya biyo bayan wani rahoton da ƙungiyar ta bayyana wanda a cikinsa ta ce a shekara bara da ta shige ta 2014.

Kamfanon aiki haƙon man fetur ɗin na Shell na Ingila da Eni na Italiya waɗanda ke gudanar da aiyyukansu a Najeriyar sun ce sun haddasa gurɓacewar muhali a wurare 553.Ƙungiyar ta ce wannan addadi da kamfanonin suka bayyana na ɗaga hankali sossai, kuma ta ce ya zama wajibi a farka daga barci tun da sauran wuri.