Guinea: Za a yankewa Moussa Camara hukunci
July 31, 2024A wannan Larabar ce ake sa ran kotun kasar Guinea ta yanke hukunci kan shari'ah tsohon shugaban kasar, Moussa Dadis Camara da wasu jami'an gwamnati da kuma dakarun soji 11, bisa zarginsu da hannu a kisan gillar mutane sama da 150 da kuma yiwa wasu gomman mata fyade.
A watan Satumbar shekarar 2009 ne aka zargi masu gadin shugaban da farwa daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnatinsa a filin wasanni da ke babban birnin kasar Conakry.
Karin bayani: Kisan kiyashi a Guinea
Camara dai ya dade ya na musanta zargin da ake masa na hannu a lamarin da ake ganin a iya yanke musu hukuncin daurin rai da rai. Sai dai dukannin wadanda ake zargi na da tsawon kwanaki 15 su daukaka kara kan hukuncin da za a yanke a shari'ar ta yau, da 'yan kasar suka dade suna zaman jira.