Guinea: ′Yan adawa sun amince su shiga zabe | Labarai | DW | 07.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guinea: 'Yan adawa sun amince su shiga zabe

'Yan adawar Guinea Konakry sun bayyana wannan matsayi nasu ne lokacin wani taron manema labarai da suka shirya a jiya Talata.

Guinea Präsident Wahlen Kandidat Cellou Dalein Diallo

A Guinea Konakry 'yan adawar kasar sun ce ba za su kaurace wa zaben shugaban kasa zagaye na fako da kasar za ta shirya ranar Lahadi mai zuwa ba, inda 'yan takara takwas da suka hada da shugaban kasar na yanzu wato Alpha Conde za su Fafata. Sun bayyana wannan matsayi nasu ne lokacin wani taron manema labarai da suka kira a yammacin jiya Talata a birnin Konakry a karkashin jagorancin Aliou Conde wani na hannun damar madugun 'yan adawar kasar Cellou Dalein Diallo.

Sai dai 'yan adawar kasar ta Guinea sun yi kira ga hukumar zaben kasar da ta gudanar da gyaran huska kan wasu kura-kurai da suka ce na tattare da tsarin zaben wadanda ka iya yin munmunan tasiri ga sakamakon karshe musammam dangane da abin da ya shafi girgam din zabe da rarraba katocin zaben dama kasasfin runfunan zabe a tsakanin yankunan kasar.

A makon da ya gabata dai 'yan adawar kasar ta guinea sun bukaci hukumar zaben kasar da ta dage zaben koda da akalla mako daya domin gudanar da wadannan gyare-gyare amma hukumar zaben kasar ta yi burus da wannan batu nasu.