1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cecekucen gabanin zabe a Guinea-Bissau

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
October 29, 2019

A Guinea-Bissau, zarge-zarge tsakanin 'yan takara sun kama hanyar kassara yakin neman zabe a daidai lokacin da ya rage makonni kalilan a gudanar da zaben shugaban kasa na ranar 24 ga watan Nuwamba.

https://p.dw.com/p/3S8VD
Kombobild  Präsidentschaftskandidaten Guinea Bissau

A Guinea-Bissau, zarge-zarge tsakanin 'yan takara sun kama hanyar kassara yakin neman zabe a daidai lokacin da ya rage makonni kimanin uku a gudanar da zaben shugaban kasa. Wannan rikicin siyasa da zargin fataucin muggan kwayoyi na neman jefa zaben na ranar 24 ga watan Nuwamba cikin hadari.

Gwamantin Guinea-Bissau ta jima da gazawa wajen yakar cin hanci da karbar rashawa da kuma fataucin miyagun kwayoyi. Hasali ma kasar ta kasance muhimmiyar cibiyar fataucin miyagun kwayoyi tsakanin Afirka da Turai. Yawancin 'yan siyasa da sojojin kasar na amfani da raunin da kasar ke da shi wajen karbar cin hanci da rashawa daga masu fataucin miyagun kwayoyi daga Kudancin Amirka. A yanzu ma dai kasar ta daina gudanar da ayyukanta na yau da kullun, inda aka rufe makarantu da jami'o'i da dama, yayin da tsarin kiwon lafiya ya lalace, kuma tsarin shari'a ya sukurkuce. Sai dai Assana Sambu, babban editan jaridar Guinea-Bissau "O Democrata" ya dora wannan komabayan kan 'yan siyasar Guinea-Bisau:

"Jama'a sun gaji da hakuri. A duk lokacin da muke ganin cewa mun kai makura, sai daya daga cikin 'yan siyasarmu, misali, shugabanmu, ya zo ya kara karaya a kan targade. Don haka komai ya ci gaba da tabarbarewa, kasarmu ta yi rarrabuwar da ba ta taba yi ba a baya. 'Yan siyasa ne ke rura wutar rikicin! "


'Yan siyasa da jam'iyyu a Guinea-Bisau sun kasa yin aiki tare, dama kuma kasar na fama da matsaloli na kabilanci da kuma addinni, lamarin da ya hana ruwa guda wajen hada gwiwa wajen kafa gwamnati. Ko da sabon zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 24 ga watan Nuwamba, ana ganin cewar shirya shi abu ne mai wahala saboda hukumomin sun koka kan rashin isasshen kudi, baya ga takaddama kan rashin sabunta rejistar masu kada kuri'a. Amma kum wata daya kafin ranar zaben da aka shirya, yarfen siyasa na ci gaba da kankama inda Firayiminista Aristides Gomes ya yi amfani da kafar facebook wajen zargin dan takara Umaru Sissoco Embaló da shirya yin juyin mulki:

Umaro Sissoco Embalo, Guinea-Bissau-Präsidentschaftskandidat
Umar Sissoco Embalo dan takarar a shugaban kasa a Guinea-BissauHoto: DW/J. Carlos

"Mun yi abin da ya kamata a yi. Dole ne mu kare jama'armu daga duk wani yunkuri na juyin mulki. Ya kamata Sissoco ya fuskanci hukuncin abin da ya aikata"


Gwamnatin Guinea-Bisau ta sanya jami’an tsaro yin sintiri kan manyan titunan Bissau babban birnin saboda tana zargin 'yan adawa da son hana gudanar da zaben shugaban kasa na ranar 24 ga Nuwamba. Tuni dan adawa Sissoco dan takarar shugaban kasa ya yi watsi da zargin da ake masa bayan da aka fara gudanar da bincike:
 
"Dukkanin abubuwan karya ne, yarfe ne kawai ba kamshin gasakiya a ciki. Gwamnatin tana so ne kawai ta nesanta kanta daga kaurin suna da ta yi a kan safarar muggan kwayoyi. Sun san cewa zan lashe zabe mai zuwa, saboda haka suke neman shafa min kashin kaji. Ba daidai ba ne a ce ina son shirya juyin mulki bayan ya dade da tube kakin janar. "

José Mário Vaz
Jose Mario Vaz Shugaban kasar Guinea-BissauHoto: DW/B. Darame


'Yan takara 12 ne suka sami damar shiga zaben shugaban kasar Guinea-Bisau, amma ana ganin cewar biyar daga cikinsu ne kawai za su iya taka rawar gani. Na farko shi ne  José Mário Vaz, mai shekaru 61, wanda ya tsaya a matsayin dan indipenda wanda ke da goyon bayan mazauna karkara. Sai Domingos Simões Pereira, wanda ke da goyon bayan gwamnati, amma ake zargi da marar hannu a safarar miyagun kwayoyi. Sai kuma Carlos Gomes Júnior wanda ya yi gaban kanshi duk da dasawa da yake yi da gwamnati, da Umaru Sissoco Embaló mai shekaru 48, tsohon Firayiministan Guinea-Bisau kuma tsohon janar na soji da kuma Nuno Gomes Nabiam mai shekaru 53, wanda ya kai zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da ya gudana a 2015. Sai dai rikice-rikice da ake fama da su a Guinea-Bisau sun sa an fara tsammanin dage zaben na shugaban kasa domin warware su cikin ruwan sanyi kafin a tsayar da sabon jadawali na zabe.