1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea-Bissau za ta samu sabbin 'yan majalisa

June 4, 2023

Zaben na cikin zabukan da ke jan hankalin kasashen duniya amma 'yan kasar na dari-dari da abin da zai iya biyo baya, duba da yadda kasar ta yi kaurin suna wajen tsunduma cikin rikici na siyasa da kuma juyin mulki.

https://p.dw.com/p/4SAv1
Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea-BissauHoto: DW

Masu zabe kimanin 900,000 na can na zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Guinea-Bissau.  Fafatawar ta fi zafi a tsakanin jam'iyyar PAIGC da ta yi kokarin wajen samun 'yan cin kan kasar da kuma Madem-G15. Masu sanya ido daga ciki da wajen kasar sama da 200 ne ke duba yadda zaben ke gudana. Ana sa ran rufe rumfunan zaben da mislain karfe biyar na yamma agogon kasar.

Rikicin da yanzu haka ya fi daukar hankalin 'yan kasar shi ne takaddmar da ta barke kan bukatar da Shugaba Embalo ya mika wa majalisar da aka rushe bara ta gyaran kudin tsarin mulki.