Guillaume Sorro ya koma birnin Abidja | Labarai | DW | 14.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guillaume Sorro ya koma birnin Abidja

Madugun yan tawayen ƙasar Cote D`Ivoire Guillaume Sorro, ya koma birnin Abidjan a ranar yau talata, inda ya ɗauki muƙamin sa, na ministan gina ƙasa, bugu da ƙari mataimakin praminista a cikin sabuwar gwamnati riƙwan ƙwarya.

Fiye da shekara guda kenan, da Guillaume Sorro ya hita daga Abidjan, dalili da ƙarancin matakan tsaro.

Jim kaɗan bayan saukar sa, ya gana da shugaban ƙasa Lauran Bagbo, da kuma Pramista Charles Konnan Banny, inda su ka tantana, a kan shirye shiryen samar da zaman lahia, a wannan ƙasa, da ke fama da rikicin tawaye, da na siyasa.

Guillaume Sorro, ya bayyana wa manema labarai gamsuwa, da batutuwan da ya tantana da shugabanin 2.

Ya kuma nunar da cewa, akwai haske, cikin sabuwar tafiyar da a ka shiga ta maido da kwanciyar hankali.

Inda, ɓangarori daban daban su ka cika alkawuran da su ka ɗauka, babu shakka, za a iya shirya zaɓen shugaban ƙasa, kamin ma, watan oktober mai zuwa, inji magudugun yan tawaye Cote D´Ivoire.