1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maduro ya ce zai murkushe 'yan adawa

Zainab Mohammed Abubakar
March 6, 2019

Shugaban adawa kuma mutumin da ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a Venezuewa Juan Guaido, ya lashi takobin cigaba da matsin lamba wa shugaba Nicolas Maduro har sai ya yi murabus

https://p.dw.com/p/3EVqf
Venezuela l Rückkehr des Interimspräsident Guaidó
Hoto: picture alliance/dpa/Agencia Brazil/M. Camargo

 

Sai dai a daya hannun Maduro ya yi alkawarin murkushe wadanta ya kira " mahaukatan tsirarun kasar" da ke kokarin ganin cewar sun kifar da gwamnatinsa..

Shugaban majalisar wakilan kasar mai shekaru 35 da haihuwa, ya samu kyakkyawar tarba jiya da ya koma gida, bayan barin kasar a wata ziyarar kwanaki 10 da ya kaiwa mukarrabansa da ke yankin kudancin Amurka.

Guaido ya komo gida ba tare da an capkeshi kamar yadda gwamnati ta sha alwashin yi ba.