Guguwar Irma ta isa gabar kogi a Florida
September 10, 2017Talla
Guguwar Irma na kara yin karfi yayin da ta ke shirin yin dirar mikiya a Florida a yau Lahadi hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma barazanar ta'adi mai yawa wanda ya tilasta kwashe jama'a daga gidajen su a wani lamari mafi girma da ba'a taba gani ba a tarihin kasar Amirka.
Mahaukaciyar guguwar wadda ta fara yin mummunan barna a yankunan gabar kogi a Kuba tana tafiyar kilomita 210 cikin sa'a guda a kudu maso gabashin Florida a cewar cibiyar nazarin guguwa ta kasar.
Guguwar ta Irma wadda hallaka akalla mutane 22 a yankin Caribbean, an yi kiyasin za ta haddasa ta'adi na biliyoyin daloli.
A halin da ake ciki an sami katsewar wutar lantarki a gidaje kusan dubu 500 a Florida sakamakon guguwar.